'Ya kamata a bai wa Van Gaal lokaci'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Van Gaal na tsaka mai wuya

Tsohon kocin Manchester United, David Moyes ya ce ya kamata kungiyar ta goyi bayan Louis van Gaal domin ya ci gaba da jan ragamar ta.

"Ya kamata Manchester United ta dinga rike manajojinta, ta goyi bayansu," in ji Moyes a hirarsa da BT Sport.

A yanzu dai United na matakin na shida a kan teburin gasar premier.

Moyes ya kara cewar "Bai kamata su zama kungiyar da ke canza koci a koda yaushe ba."

Moyes ya maye gurbin Sir Alex Ferguson a shekarar 2013, amma kuma aka kore shi bayan watanni 10.

Van Gaal ne ya maye gurbin Moyes a Old Trafford a watan Mayun 2014.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cikin watanni 10 United ta kori