Ba zan sauya salon horas da 'yan wasa ba — Van Gaal

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Sau uku Manchester United na shan kashi a hannun Swansea tun da Van Gaal ya zama kociya.

Kociyan Manchester United Louis van Gaal ya ce dole ya ci gaba da salon da yake bi wajen horas da 'yan wasansa domin ya inganta yadda suke murza leda.

Mista van Gaal ya ce babu wani siddabaru da zai iya yi domin kawo sauyi a kungiyar.

Kungiyar ba ta yi nasara ko da sau daya ba a cikin wasanni takwas da ta buga, ciki har da wasanni shida na Gasar Premier.

Hakan ya sa ta koma matsayi na shida a teburin gasar Premier, kuma aka fitar da ita daga gasar cin Kofin Zakarun Turai.

A ranar Asabar suka fafata da Swansea, kulob din da ya bai wa United kashi sau uku tunda aka nada Van Gaal a matsayin kociya.

Van Gaal ya ce, "Babu wani siddabaru da zan iya yi a kan kulob din, mun ga abin da ya faru kuma za mu ga yadda za a ingata wasanmu."