Arsenal ta ci gaba da zama a kan teburin Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburi

Arsenal ta ci Newcastle daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 20 da suka kara a ranar Asabar a filin wasa na Emirates.

Laurent Koscielny ne ya ci wa Arsenal kwallon saura minti 18 a tashi daga fafatawar.

Da kuma wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier da maki 42.

Ita kuwa Newcastle United tana nan a matakinta na 18 da maki 17 a kan teburin gasar.

Arsenal za ta karbi bakuncin Sunderland a wasan gasar kofin FA a ranar Asabar tara ga watan Janairu.