Ina son na horas da Liverpool - Gerrard

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Steven Gerrard na sa ran yin ritaya daga taka-leda a bana

Tsohon kyaftin din Liverpool, Steven Gerrard, ya ce yana shirin ya koma kungiyar a matsayin kociya idan ya yi ritaya daga taka-leda.

Gerrard wanda ya lashe kofuna 10 a Liverpool, ya koma Los Angeles Galaxy ta Amurka da murza-leda a bara.

Dan wasan ya ce ba shi da tabbacin cewar ko a shekarar nan zai daina buga kwallo a matsayin dan wasa.

Gerrard ya kuma ce ya tattauna da kociyan Liverpool Jurgen Klopp da kuma kungiyar idan tana da sha'awar ya koma a matsayin mai horas da 'yan wasa.

Ya kuma kara da cewar tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamba ya ke sa ran yin ritaya, kuma duniya za ta sani, a kuma lokacin ne ya ke sa ran shaidarsa ta zama kociya za ta kammala kashi 75 cikin dari.