Oliseh ya bayyana 'yan wasan Super Eagles 23

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption Rwanda ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka a cikin watan Janairu

Kociyan tawagar kwallon kafa na Nigeria, Sunday Oliseh ya fitar da sunayen 'yan wasa 23 na Super Eagles masu taka leda a gida da za su wakilci kasar a kofin nahiyar Afirka.

Rwanda ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke murza leda a gida, inda za a fara a ranar Asabar 16 ga watan Janairu.

Nigeria tana rukuni na uku da ya kunshi Tunisia da Guinea da kuma Nijar wadanda za su fafata a Stade Regional Nyamirambo, Kigali.

Tawagar Nigeria ta isa kasar Afirka ta kudu domin buga wasan sada zumunta da Angola da kuma Cote d'Ivoire domin shirin tunkarar gasar ta Afirka.

Ga jerin sunayen da Oliseh ya fitar:

Masu tsaron raga: Ikechukwu Ezenwa (Sunshine Stars); Olufemi Thomas (Enyimba FC); Okiemute Odah (Warri Wolves)

Masu tsaron baya: Austin Oboroakpo (Abia Warriors); Kalu Orji Okogbue (Enugu Rangers); Jamiu Alimi (Shooting Stars); Mathew Etim (Enugu Rangers); Chima Akas (Sharks FC); Stephen Eze (Sunshine Stars); Christopher Madaki Maichibi (Giwa FC); Samson Gbadebo (Lobi Stars)

Masu buga tsakiya: Ifeanyi Mathew (El-Kanemi Warriors); Paul Onobi (Sunshine Stars); Usman Mohammed (FC Taraba); Yaro Bature (Nasarawa United); Bartholomew Ibenegbu (Warri Wolves); Ibrahim Attah Salau (Shooting Stars)

'Yan wasan gaba: Osas Okoro (Enugu Rangers); Ezekiel Bassey (Enyimba FC); Tunde Adeniji (Sunshine Stars); Bright Onyedikachi (FC IfeanyiUbah); Chisom Chikatara (Abia Warriors); Prince Aggrey (Sunshine Stars)