Chelsea ta doke Crystal Palace da ci 3-0

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Chelsea ta koma matsayi na 14 a kan teburin Premier

Chelsea ta samu nasara a kan Crystal Palace, bayan da ta zura mata kwallaye 3-0 a gasar Premier wasan mako na 20 da suka kara a Selhust Park ranar Lahadi.

Chelsea ta fara cin kwallon farko ta hannun Oscar a minti na 29 da fara tamaula, kuma da haka aka tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Chelsea ta kara kwallo ta biyu ta hannun Willian, sannan Costa ya zura ta uku mintuna shida tsakanin da aka ci kwallo ta biyu.

Da wannan sakamakon Chelsea ta koma matsayi na 14 a kan teburin Premier da maki 23, inda Crystal Palace na nan a matakinta na bakwai a kan teburin da maki 31.

Chelsea za ta karbi bakuncin Scunthorpe United a gasar kofin FA a ranar Lahadi, inda Crystal Palace za ta ziyarci Southampton a kofin na FA a ranar Asabar.