Zan so na ci gaba da horas da Valencia - Neville

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Garry Neville tsohon dan wasan Manchester United ne

Gary Neville ya ce yana fatan ci gaba da horas da 'yan wasan Valencia bayan da suka tashi 2-2 da Real Madrid a gasar La Liga ranar Lahadi.

Neville -- wanda ya sanya hannu kan kwantiragin watanni shida da Valencia -- ya ce ba ya zaton yana da makoma a fagen horas da kwallon kafa a gaba.

Amma kuma ana tashi daga karawar suka yi da Madrid sai ya ce ba ya tsammani zai daina aikin kociya daga nan zuwa shekaru 15 ko 20 masu zuwa.

Neville ya samu maki uku daga cikin wasannin gasar La Liga hudu da ya yi tun komawarsa Valenci.

Valencia -- wadda ke mataki na 10 a kan teburin La Liga -- za ta ziyarci Real Sociedad a wasan mako na 19 a gasar.