Jamie Vardy zai yi jinyar makonni biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamier Vardy ya ci kwallaye 15 a gasar Premier

Dan kwallon Leicester City, Jamie Vardy zai yi jinya ta mako daya zuwa biyu kafin ya dawo fagen taka-leda.

Vardy yana kan ganiyarsa a wasan kwallon kafa a gasar Premier bana, inda ya ci kwallaye 15 a gasar, haka kuma ya sa Leicester ke mataki na biyu a kan teburin gasar.

Dan wasan ya kuma buga wa kungiyar wasanni 24 a fafatawar da take yi a bana.

Vardy yana daga cikin 'yan wasan tawagar Ingila da suka samarwa da kasar tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a shekarar nan.

Dan kwallon ya buga wasan Premier da Leicester ta tashi wasa babu ci da Bournemouth a ranar Asabar.