Turan da Vidal za su fara yi wa Barca wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ta sayo Vidal daga Sevilla, sannan ta dauko Turan daga Atletico Madrid

Aleix Vidal da Arda Turan za su fara buga wa Barcelona wasan farko a cikin makon nan, bayan da wa'adin hukuncin dakatar da kungiyar daga sayen 'yan kwallon kafa makonni 14 ya kare.

Vidal mai tsaron baya wanda Barca ta dauko daga Sevilla kan kudi fam miliyan 13 zai saka riga mai lamba 22.

Shi kuwa Turan mai wasan tsakiya wanda ya koma Barca daga Atletico Madrid zai saka riga mai lamba bakwai ne.

Dukkansu 'yan wasan biyu sun cancanci su buga gasar Copa del Rey da Barcelona za ta kara da Espanyol a ranar Laraba.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ce ta dakatar da Barcelona daga sayen 'yan wasan kwallon kafa, bayan da aka samu kungiyar da laifin karya ka'idar sayen matasan 'yan kwallo.

Duk da hana Barcelona sayen 'yan wasa a shekarar 2015 da aka yi, bai hana ta lashe kofin La Liga da na Copa del Rey da na Zakarun Turai da Zakarun nahiyoyin duniya da kuma Super Cup.

Barcelona tana mataki na biyu a kan a kan teburin La Liga da maki 39.