Adidas ya soki 'salon wasan' United

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Van Gaal na tsaka mai wuya

Shugaban kamfanin yin kayan kwallo-Adidas, Herbert Hainer ya soki salon wasan Manchester United.

Shugaban Adidas wanda ke daukar nauyin yi wa United rigar kwallo ya ce 'ba sa ganin abin da suke so' a Old Trafford.

Adidas na biyan United fam miliyan 75 a duk shekara a yarjejeniyar da suka kulla.

Hainer ya shaidawa jaridar Suddeutsche Zeitung ta Jamus cewa "kasuwancinmu da United na tafiya yadda ya kamata, amma akwai shakku kan yadda kungiyar ke murza leda."

Kocin United, Louis van Gaal na shan suka daga wajen magoya bayan kungiyar da tsaffin 'yan wasan da kuma kafafen yada labarai.

A yanzu haka an fitar da United daga gasar zakarun Turai, sannan kuma ita ce ta shida a teburin gasar Premier.