Kevin-Prince Boateng ya sake komawa AC Milan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kevin-Prince Boateng ya koma kulob din Milan a karo na biyu

Dan kwallon tawagar Ghana, Kevin-Prince Boateng, ya sake komawa AC Milan a matsayin maras yarjejeniya da wata kungiya.

Kulob din AC Milan ya ce ya kulla yarjejeniya da Kevin-Prince Boateng domin ya buga masa wasanni har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2016.

A watan Mayun 2015 ne Schalke ta dakatar da shi daga buga mata kwallon kafa, inda ya koma yin atisaye a Milan tun daga watan Satumbar da ya wuce.

Boateng ya yi kokari ya koma Sporting Lisbon da murza-leda amma hakan bai yi wu ba, kuma a watan Disambar 2015 Schalke ta katse kwantiraginta da dan wasan.

Schalke ta dakatar da Boateng ne a inda ta ce babu yarda da juna tsakaninta da dan kwallon.

Boateng ya fara wasa aro a Milan daga Genoa a 2010, sannan ya koma da taka leda kacokan a 2011.