Rooney ne ya fi yin fice a kwallon kafa a Ingila

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wayne Rooney dan kwallon Manchester United kuma kyaftin din Ingila

An bayyana Wayne Rooney a matsayin dan kwallon kafar da ya fi yin fice a Ingila a shekarar 2015 da magoya bayan tawagar suka zaba.

Rooney mai murza-leda a Manchester United ya samu kuri'u kaso 37 cikin dari, kuma karo na hudu kenan yana lashe kyautar.

Dan wasan kuma kyaftin din Ingila ya ci mata kwallaye biyar a shekarar da ta wuce a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.

Hakan ne ya kuma sa ya dara Sir Bobby Charlton a matasyin wanda ya fi ci wa Ingila kwallaye a tarihi.

Dan wasan Tottenham, Harry Kane shi ne ya yi na biyu, sai golan Manchester City, Joe Hart ya yi na uku.

Mai tsaron ragar Stoke City, Jack Butland ne ya lashe kyautar matashin dan wasa mai shekara 21 da ya fi haskakawa.