An kashe babban jami'in NFF a Abuja

Hakkin mallakar hoto WhatsApp
Image caption Margayi Ibrahim Abubakar

'Yan fashi da makami sun hallaka wani babban jami'in a hukumar kwallon Najeriya, NFF Malam Ibrahim Abubakar a gidansa da ke Abuja.

Malam Abubakar shi ne babban jami'i mai karbar baki a hukumar NFF.

Tsohon dan kwallon Arsenal, Nwankwo Kanu ya bayyana kashe Abubakar a matsayin "mugun labari mara dadi."

Rahotanni sun ce margayin ya rasu ya bar matarsa da 'ya'ya uku.

Nan gaba a ranar Laraba za a yi jana'izarsa a Kaduna.

Kakakin Super Eagles, Oluwatoyin Ibitoye shi ma ya bayyana kaduwarsa game da kashe Abubakar.