Liverpool ta dauko Marko Grujic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana mataki na takwas a kan teburin Premier da maki 30

Liverpool ta sayo Marko Grujic kan kudi sama da fam miliyan biyar daga kungiyar Red Star Belgrade kan kwantiragin shekara hudu.

Dan wasan mai shekara 19, zai ci gaba da wasa a Red Star Belgrade a zaman aro, kafin ya dawo murza-leda a Liverpool a ranar daya ga watan Yuli.

Liverpool ta doke Anderlecht da Stuttgart da CSKA Moscow da kuma Zenit St Petersburg da suma suka yi zawarcinsa.

Grujic wanda ke buga wa tawagar Serbia tamaula, ya ci kwallaye biyar daga wasanni 22 da ya yi wa Red Star Belgrade.

Kuma dan wasan ne na farko da Jurgen Klopp ya sayo tun sanda ya koma Liverpool da horas da tamaula a cikin watan Oktoba.