Zidane ba ya so a kwatanta shi da Guardiola

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption A ranar Litinin Real Madrid ta nada Zidane a matsayin kocin rikon kwarya

Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane ya ce bai kamata a dinga kwatanta shi da mai horas da Bayern Munich, Per Guardiol ba domin akwai tazara mai tsawo a tsakaninsu.

Zidane -- tsohon dan kwallon Real Madrid -- ya maye gurbin Rafael Benitez a ranar Litinin, abin da ya sa karan shi ya kai tsaiko kamar na Guardiola sanda yana Barcelona.

Sai dai kuma Zidane ya ce a daina kwatantashi da Guardiola domin ya samu gagarumar nasarori da yawa a fagen murza-leda.

Guardiola -- tsohon dan wasan Barcelona -- ya fara horas da karamar kungiyar kafin daga baya ya jagoranci babbar Barca inda ya lashe kofuna da kyautuka da dama.

A shekara hudu da ya yi da Barcelona Guardiola ya lashe kofuna 14 ciki har da na kofin Zakarun Turai da La Liga da Copa del Rey a kakar farko da ya jagoranci kungiyar.

Zidane, dan kasar Faransa, ya horas da karamar kungiyar Madrid, wanda aka nada a matsayin kociyan riko domin maye gurbin Rafael Benitez.