Traore zai yi jinyar makonni goma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Traore zai yi jinyar makonni goma.

An dakatar da dan wasan gaba na Aston Villa Adama Traore, daga buga tamaula har na tsawon makonni goma bayan da ya karye a kafarsa ta dama.

Traore mai shekara 19, ya ji rauni ne lokacin da kulob dinsa ke karawa da Sunderland a ranar Asabar, yayin da yake kokarin taimakawa Carles Gil cin kwallon da ya zura.

Dan wasan dan kasar Sipaniya, ya koma kulob din Villa ne daga Barcelona kan kudi fam miliyan bakwai a lokacin bazarar da ta gabata, ya kuma ci kwallo daya a wasanni goman da ya buga.

Manajan kulob din Remi Garde, ya ce kungiyar na fuskantar kalubale tun farkon wannan kakar wasan, don haka tana bukatar sabbin 'yan wasa don farfado da shi.