Za a sanar da gwarzon dan kwallon Afrika na 2015

Image caption Sau hudu Yaya Toure ya lashe zaben.

Nan gaba a ranar Alhamis (yau) za a sanar da gwarzon dan kwallon Afrika na shekarar 2015 da hukumar kwallon kafar Afrika CAF za ta zaba.

A Abuja babban birnin Najeriya ne za a gudanar da bikin.

'Yan takarar zaben guda uku sun hada da Yaya Toure da Dede Ayew da kuma Pierre-Emerick Aubameyang.

Wannan ne karo na biyar da Yaya Toure ya kasance cikin 'yan takarar inda kuma ya lashe kyautar sau hudu.

Sannan akwai wasu kyautuka da za a bayar a lokacin bikin, ciki har da na tauraruwar kwallon mata a Afrika da dai sauransu.