United ta yi wa Januzaj kiranye

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Januzaj ba ji dadin zamansa a Jamus ba

Manchester United ta yi wa dan kwallonta Adnan Januzaj, kiranye bayan da ya tafi a matsayin aro a Borussia Dortmund.

United ta bukaci dan wasan mai shekaru 20 ya komo Old Trafford, saboda ba a saka shi a wasa a Dortmund.

Sau 12 kacal Januzaj ya buga wa Dortmund kwallo a kakar wasa ta bana.

Kafin ya bayar da shi aro, dan kwallon ya murza wa United leda a watan Agusta.

Kwangilarsa za ta kare ne a Old Trafford a shekara ta 2018.