Coutinho zai yi jinya har zuwa Fabrairu

Image caption Coutinho zai yi makonni biyu yana jinya

Akwai yiwuwar dan wasan tsakiya na kulob din Liverpool Philippe Coutinho, ba zai iya wani wasa ba a cikin watan Janairu, sakamako raunin da ya ji a gwiwarsa a wasan da kulob dinsa ya fafata da Stoke.

Shi ma dan wasan baya Dejan Lovren da kuma Kolo Toure sun ji rauni a cinya, amma ba za su dade suna jinya ba.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp, ya ce duk da cewa raunin da Coutinho ya ji, ya fi na Lovren da Kolo amma ba wanda zai buga wasan da kulob din zai yi a ranar Juma'a.

Ya ce "Kolo zai buga wasa a wani makon, Dejan kuma zai dawo fagen wasa bayan an kara da Manchester United, yayin da shi kuwa Coutinho zai yi jinyar kusan makonni biyu."