Ba zan yi takarar FIFA ba — Platini

Hakkin mallakar hoto Rianovosti
Image caption A shekarar 2015 ne FIFA ta dakatar da Mista Platini daga shiga harkokin wasannin kwallo.

Michel Platini ya ce ba zai tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ba da za a yi a watan Fabrairu.

A shekarar da ta gabata ne aka dakatar da shugaban Fifa Sepp Blatter da shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini daga shiga al'amuran da suka shafi tamaula na tsawon shekaru takwas.

Kwamitin kula da da'a na hukumar FIFA ne ya dauki wannan mataki, bisa zarginsu da hannu a cin hanci da rashawa.

Duk da cewa sun daukaka kara mista Platini ya ce lokacin da aka sanya don yin zaben na 26 ga watan Fabrairu ya karato ta yadda ba zai iya tsayawa takarar ba.

Ya ce, "Lokacin ya min kadan. Bani da lokacin da zan fafata da sauran 'yan takara, ba a bani lokacin gwada bajinta ta ba."