Ba za mu sayar da Carroll ba - Bilic

Image caption Slaven Bilic ya ce ba za su sayar da Carroll ba.

Kociyan West Ham Slaven Bilic ya kawar da yiwuwar sayar da dan wasan gaba Andy Carroll lokacin saye da sayar da 'yan wasa na watan Janairu.

Carroll ya jima yana fama da jinya a wannan kakar wasan kuma yana ta samun tayin komawa Sunderland ko tsohon kulob dinsa Newcastle.

Amma a baya-bayan nan ya ci kwallo biyu a wasanni biyu.

Koci Bilic ya ce, "Bama son sayar da shi, kulob din bai shirya sayar da shi ba."