Babu inda Cristiano zai je — Zidane

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ronaldo na ci gaba da haskakawa a Real Madrid

Cristiano Ronaldo ba zai bar Real Madrid ba a nan kusa, in ji sabon kocinsa Zinedine Zidane, wanda ya bayyana shi a matsayin 'ruhin' kungiyar.

Zidane ya bayyana haka ne a taronsa na manema labarai a karon farko, tun bayan da aka nada shi kocin Real.

"Cristiano ba zai bar mu ba," in ji Zidane.

Ya kara da cewa "Shi ne ruhin tawagar.Babu inda za shi."

Ronaldo ya bar United a shekara ta 2009, inda ya koma Real a kan fan miliyan 80.

Ya kafa tarihi a Real, inda ya zura kwallaye 323 a kungiyar a yayin da ya shiga gaban Raul.