Arsenal ta cire Sunderland daga kofin FA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ta kai wasan gaba a gasar cin kofin FA na Ingila

Arsenal ta kai wasan zagayen gaba a kofin FA, bayan da ta doke Sunderland da ci 3-1 a karawar da suka yi a Emirates a ranar Asabar.

Sunderland ce ta fara cin kwallo ta hannun Jeremain Lens, daga nan Arsenal wadda ke rike da kofin ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Joel Campbell.

Alex Oxlade-Chamberlain ya buga kwallo ta bugi turke, kuma nan da nan Aaron Ramsey wanda ya shiga wasan daga baya ya ci ta biyu, sannan Olivier Giroud ya kara ta uku a raga.

Rabonda Arsenal a doke ta a gasar cin kofin FA tun ranar da Blackburn ta ci ta 1-0 a cikin watan Fabrairun 2013 a Emirates, kuma wannan shi ne wasa na 13 da ta lashe a jere a gasar.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka buga a ranar Asabar din:

 • Wycombe 1 - 1 Aston Villa
 • Birmingham 1 - 2 Bournemouth
 • Brentford 0 - 1 Walsall
 • Bury 0 - 0 Bradford
 • Colchester 2 - 1 Charlton
 • Doncaster 1 - 2 Stoke
 • Eastleigh 1 - 1 Bolton
 • Everton 2 - 0 Dag & Red
 • Hartlepool 1 - 2 Derby
 • Huddersfield 2 - 2 Reading
 • Hull 1 - 0 Brighton