Ba za mu sayar da Kane ba - Pochettino

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham tana mataki na hudu a kan teburin Premier

Kociyan Tottenham, Mauricio Pochettino, ya sake nanata cewar Harry Kane ba na sayarwa ba ne.

Pochettino ya ce ba zai yi mamaki ba idan Real Madrid ta zama daya daga cikin kungiyoyin da ke son daukar dan kwallon.

Kociyan ya kara da cewar ba sa son sayar da Kane, shi ma kuma dan wasan ba ya son ya barin Tottenham a yanzu.

Kane mai shekara 22, ya ci wa kungiyar kwallaye 13 a raga a gasar Premier, kuma hakan ne ya taimaka mata kaiwa matsayi na hudu a kan teburin gasar.

Kane ya fara murza-leda a Tottenham tun yana da shekara 11, kuma Pochettino ba ya fatan dan kwallon zai bi sahun Gareth Bale da Luka Modric wadanda suka koma Madrid da taka-leda daga kungiyar.