Van Gaal zai sayo 'yan wasa a Janairun nan

Hakkin mallakar hoto rex features
Image caption Van Gaal ya ce a watan Janairu ba za a samu dan wasa mai kwari na sayarwa ba

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal, na son ya kara karfin kungiyar a Janairun nan, amma ya ce ba lokaci ne da za a iya yin kasuwanci ba yanzu.

United tana mataki na biyar a kan teburin Premier, kuma a makon jiya ne ta doke Swansea wanda hakan ya sa ta kawo karshen kasa lashe wasa a karawa takwas da ta yi a jere a baya.

United din za ta fafata da Sheffield United a gasar cin kofin FA a ranar Asabar.

Kociyan ya ce da zarar an samu dama to lallai kam zai sayo karin 'yan wasa, amma wannan lokacin bai dace a dauko dan kwallo ba domin kakar wasa ba ta kare ba.

Van Gaal na shan suka kan salon yadda yake horas da tamaula a OldTrafford a wajen masu goyon bayan United da tsofaffin 'yan wasanta da 'yan jaridu.