Wa zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Litinin za a bayyana wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2015

A ranar Litinin ne hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, za ta bayyana wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na shekarar 2015.

'Yan wasa uku ne ke yin takara da suka hada da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da Neymar, wandanda a cikinsu za a zabi wanda ya lashe kyautar ta Ballon d'Or.

Wannan ce shekara ta takwas a jere da Ronaldo, dan kwallon Real Madrid, da dan wasan Barcelona Messi ke shiga cikin 'yan takara.

Wannan shi ne karon farko da Neymar ya shiga cikin jerin 'yan takara uku na karshe da za a zabi wanda ya fi yin fice a fagen tamaula a duniya.

Ronaldo dan kwallon Real Madrid shi ne wanda ya lashe kyautar 2013 da kuma 2014, ya kuma fara lashe kyautar ne a 2008.

Lionel Messi kuwa ya karbi kyautar ne tun daga shekarar 2009 da 2010 da 2011 da kuma 2012.

Haka kuma Fifa za ta karrama macen da ta fin kwazo a 2015 da matashin dan wasan da ya fi haskakawa da tawagar kwallon kafa da ta bunkasa da sauran kyautukan da za a bayar.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, za ta yi bikin karrama wadanda suka yi fice a fagen tamaula a kasaitaccen biki a Zurich a ranar Litinin.