Dan Kanawa da Alin Tarara sun tashi ba kisa

Image caption Dan Kanawa da Alin Tarara wannan takawar babu kisa

A wasan damben gargajiya da aka yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria an dambata a wasanni da dama.

Cikin karawar da aka yi har da wadda aka fafata da Dan Kanawa daga Kudu da Alin Tarara daga Arewa, turmi biyu kacal suka taka aka raba damben kuma babu kisa.

Danben da aka fi yin gumurzu shi ne tsakanin Sanin Kwarkwada daga Kudu da Shagon Alhazai mai kura daga Arewa, koda yake turmi uku suka yi babu wanda ya fadi a kasa.

Wasan da aka yi kisa a ranar ta Lahadi shi ne wanda Shagon Lawwalin Gusai daga Arewa ya kashe Ibrahin Bako daga Kudu, da kuma fafatawar da Shagon Kyallu daga Arewa ya kashe Bahagon Dakakin Dakaka daga Kudu a turmi na biyu.

Karawar da aka yi tsakanin Bahagon Dogon Auta daga Kudu da Dan Aliyu kanin Aminu Langa Langa daga Arewa babu kisa, kuma sun yi wasan ne cikin tsanaki domin dukkansu sun san junansa a wasan dambe.

An kuma sa zare tsakanin Bahagon Sanusi Dan Auta daga Arewa da Shagon Autan Sikido daha Kudu, kuma turmi uku suka yi babu kisa aka raba su.

Karawar da ba ta yi armashi ba kuma babu kisa ita ce tsakanin almajirin Taye daga Kudu da Dogon Na Manu daga Arewa, domin 'yan kallo ne da kansu suka ce ba sa son wasan.