'Kallon wasan Man United ya zama gundura'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United tana mataki na biyar a kan teburin Premier

Paul Scholes ya ce kallon wasannin da United ke buga wa ya zama abin gundura kuma da zarar ka kalli 'yan wasa da Louis van Gaal za ka gane hakan.

United ta doke Sheffield United da ci 1-0 a gasar cin kofin FA da suka kara ranar Asabar, kuma karo na 10 kenan da United din ba ta iya cin kwallo a minti na 45 din farko.

Scholes ya fada a wata kafar yada labarai cewar kullum magoya bayan United ba sa yin na'am da salon wasan da ta ke takawa.

Tsohon dan wasan Manchester United ya kara da cewar duk lokacin da kazo kallo sai ranka ya baci domin babu wani salon wasan da zai burge ka.

United din tana mataki na biyar a kan teburin Premier, kuma kwallaye 10 ta zura a raga a karawa 10 da ta yi a Old Trafford.