Zidane ya fara jagorantar Madrid da kafar dama

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Real Madrid ta doke Deportivo 5-0 a gasar La Liga a ranar Asabar

Sabon kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane ya jagoranci kungiyar wasan farko, inda suka doke Deportivo La Coruna a gasar La Liga a ranar Asabar.

Real Madrid din ta doke Deportivo La Coruna ne da ci 5-0 a karawar da suka yi a Bernabeu wasan gasar mako na 19.

Karim Benzema ne ya fara ci wa Real Madrid kwallo kuma ta dari da ya ci a gasar La Liga, sai Gareth Bale da ya ci uku rigis a wasan, kuma Benzema ya ci ta biyu kuma ta biyar a karawar.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta hada maki 40 tana kuma mataki na uku a kan teburin gasar Spaniyar.

Zidane ya maye gurbin Rafael Benitez wanda ya jagoranci Madrid watanni bakwai kacal, kuma a lokacin ya yi wasanni 25 ya cinye fafatawa 17 aka doke shi sau biyar sannan ya yi canjaras a karawa uku.

Benitez din ya kasa lashe manyan wasannin hamayya da Madrid ta buga da Villareal da Sevilla da kuma Barcelona, kuma ta raba maki tsakaninta da Atletico Madrid da Valencia.