Za a yi saye da sayarwar 'yan wasa - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal tana mataki na daya a kan teburin gasar Premier

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, na fatan kammala sayo Mohamed Elneny a cikin makon nan, kuma kungiyoyin Premier za su sayo 'yan wasa da dama.

Wenger na daf da dauko Elneny mai taka-leda a Basel, kuma kociyan ya ce sauran kungiyoyin gasar Premier ma za su dauko 'yan wasa domin kara karfin wasannin da suke yi.

Tsohon dan kwallon Arsenal, Benik Afobe mai wasa a Wolves ya koma buga tamaula a Bournemouth kan kudi fam miliyan 10, shi ne dan wasan da aka sayo mafi tsada a Janairun nan.

Dan wasan da Chelsea ta sayo daga Fiorentina, Juan Cuadrado, daf da za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a Janairun 2015 shi ne wanda aka dauka mafi tsada a lokacin.

An yi hada-hadar sayen 'yan wasan tamaula a Premier da ta kai kudi fam miliyan 130 a shekarar 2015.

Sai dai kuma hakan bai kai kudaden da aka kashe na fam miliyan 225 wajen dauko 'yan wasa shekarar 2011.