Da kyar Bony ya sake dawowa Swansea

Hakkin mallakar hoto Huw Evans Picture Agency
Image caption Bony ya koma Manchester City a Janairun 2015

Kocin rikon kwarya na Swansea, Alan Curtis, ya ce da wuya idan Wilfried Bony zai sake dawowa kungiyar domin murza-leda a watan nan na Janairu.

Bony dan kwallon tawagar Ivory Coast, ya koma Manchester City daga Swansea City a Janairun 2015, kuma ana rade-radin zai koma kungiyar ne wadda take mataki na 17 a kan teburin Premier.

Curtis -- wanda aka ba shi jan ragamar Swansea City zuwa karshen kakar bana -- ya ce suna da bukatar sayo dan wasa mai cin kwallo a raga a watan Janairun nan.

Bony wanda ya koma City da murza-leda kan kudi fam miliyan 28 kan kwantiragin shekara hudu da rabi ya ci kwallaye takwas a wasanni 23 da ya buga.

Andre Ayew da Bafetimbi Gomis sune masu ci wa Swansea City kwallaye, kuma kowannensu ya ci shida a gasar Premier.