Wasannin Man United na gundura ta - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester United tana mataki na biyar a kan teburin Premier

Kociyan Manchester United Louis van Gaal ya ce wasu wasannin da kulob din ke bugawa a bana suna gundurarsa.

Kociyan ya ce akwai wasu wasannin da yake jin dadin yadda ake yi da akwai kuma wadanda suke gundursa har ma su saka masa bacin rai.

Van Gaal ya ce wasu lokuta yana takaicin kasa cin kwallo duk da cewa suna taka rawar gani kan abokan hamayyarsu, amma haka kwallo ta gada.

Magoya bayan United sun yi wa 'yan wasa ihu a karawar da suka doke Sheffield United 1-0 a gasar cin kofin FA a ranar Asabar.

United tana mataki na biyar a kan teburin Premier, za kuma ta buga da Newcastle United a gasar Premier ranar Talata a St James' Park.