Ba zan koma Arsenal ba - Aubameyang

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Aubameyang Gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2015

Dan kwallon Borussia Dortmund, Pierre-Emerick Aubameyang, ya ce yana jin dadin taka leda a Jamus ba zai koma Arsenal ko Barcelona da taka leda ba.

Aubameyang, dan kasar Gabon gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2015, ya ci kwallaye 18 a wasanni 17 da ya buga a gasar Bundesliga.

A hirar da ya yi da wata kafar yada labarai Sport Bild ya ce yana ya lashe kyautuka da yawa a Dortmund, saboda haka zai ci gaba da buga wasannisa a Jamus.

A karshen kakar wasan 2020 ce yarjejeniyar da Aubameyang ya kulla da Dortmund za ta kare, ya kuma koma kungiyar ne daga Saint-Etienne a 2013.

Ana ta rade-radin cewar Arsenal tana son ta sayo dan kwallon domin ya taka mata leda a Emirates.