An umarci Cardoso ya horas da Cape Verde

Hakkin mallakar hoto khaled desoukt getty
Image caption Cape Verde ta halarci gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2015

Hukumar kwallon kafa ta tsibirin Cape Verde, ta umarci Felisberto Cardoso da ya horas da tawagarta, bayan da Rui Aguas ya ajiye aikin.

Cardoso ya yi mataimakin koci karkashin Aguas wanda ya kai tsibirin gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Equatorial Guinea a 2015.

Shugaban hukumar kwallon kafar Cape Verde, Victor Osorio ya ce sun yi hakan ne domin dorawa a kan inda Aguas ya tsaya da aikin.

Aguas ya ajiye aikin horas da Cape Verde sakamakon takaddama kan kin biyansa albashi.

Kociyan yana bin bashin albashin watanni shida