Congo ta kulla yarjejeniya da Lechantre

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lecantre ya horas da tawagar kwallon Kamaru da ta Mali

Hukumar kwallon kafa ta Congo ta ce ta kulla yarjejeniyar daukar Pierre Lechantre domin ya zama kociyan tawagarta.

Lechantre dan kasar Faransa zai saka hannu ne a kan yarjejeniyar da suka kulla a mako mai zuwa.

Kociyan zai maye gurbin Claude Le Roy wanda ya yi ritaya daga aikin a cikin watan Nuwamba.

Lechantre mai shekara 65, ya horas da Kamaru da Mali kuma kungiya ta karshe da ya jagoranta ita ce Al Ittahad Tripoli ta Libya.