Liverpool za ta karbi bakuncin Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana mataki na daya a kan teburi, Liverpool kuwa tana matsayi na takwas

Arsenal za ta ziyarci Liverpool a gasar cin kofin Premier wasan mako na 21 kuma karo na biyu da za su fafata a tsakaninsu a ranar Laraba.

A wasan farko da suka buga a filin wasa na Emirates cikin watan Agusta a gasar bana, sun yi canjaras.

Wannan ce karawa ta 184 da za su yi a gasar Premier, inda Liverpool ta ci wasanni 70, Arsenal ta samu nasara a karawa 64 suka yi canjaras sau 49.

Arsenal tana mataki na daya a kan teburin gasar da maki 42, inda Liverpool ke da maki takwas da maki 30.

Ga sauran wasannin da za a buga a gasar ta Premier:

  • Chelsea vs West Brom
  • Man City vs Everton
  • Southampton vs Watford
  • Stoke vs Norwich
  • Swansea City vs Sunderland
  • Liverpool vs Arsenal
  • Tottenham vs Leicester City