Liverpool da Arsenal sun tashi 3-3

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arsenal tana nan a mataki na daya a kan teburin Premier

Liverpool da Arsenal sun tashi wasa 3-3 a gasar cin kofin Premier karawar mako na 21 da suka fafata a Anfield.

Liverpool ce ta fara zura kwallo ta hannun Firmino a minti na 10 da fara wasan, inda Ramsey ya farke wa Arsenal minti hudu tsakani.

Firmino ne dai ya kara ci wa Liverpool kwallo ta biyu, Arsenal ta kara farke wa ta hannun Giroud.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Giroud ya ci wa Arsenal ta uku, Liverpool ma ta farke ta hannun Allen.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi Chelsea ta tashi 2-2 da West Brom, Manchester City da Everton suka buga canjaras 0-0, sai Southampton da ta ci Watford 2-0.

Stoke City kuwa 3-1 ta ci Norwich City, Swansea tasha kashi a hannun Sunderland da ci 4-2 da karawar da Leicester City ta samu nasara a kan Tottenham da ci daya mai ban haushi a filin wasa na White hart Lane.

Ga sakamakon wasannin da aka yi:

  • Chelsea 2 - 2 West Brom
  • Man City 0 - 0 Everton
  • Southampton 2 - 0 Watford
  • Stoke City 3 - 1 Norwich City
  • Swansea City 2 - 4 Sunderland
  • Tottenham 0 vs - 1 Leicester