Carroll zai yi jinyar makonni shida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Ham United tana mataki na biyar a kan teburin Premier

Dan kwallon West Ham United, Andy Carroll, zai yi jinyar makonni shida.

Dan wasan mai shekara 27 ya ji rauni ne a minti na 15 a gasar Premier a karawar da suka doke Bournemouth 3-1 ranar Laraba.

Carroll ya ci wa West Ham kwallaye biyu a wasanni hudu da ya buga mata, tun sanda ya dawo daga jinyar makonni bakwai da ya yi.

West Ham tana mataki na biyar a kan teburin Premier da maki 35, za kuma ta ziyarci Newcastle United a ranar Asabar a wasan mako na 22.