Arsenal ta sayi Mohamed Elneny

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wenger ya ce Elneny zai buga fafatawar da za su yi ranar Lahadi.

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya tabbatar da cewa kulub din yasayi dan wasan FC Basel, Mohamed Elneny.

Rahotanni na cewa an sayi elneny ne mai shekaru 23 a kan kusan fan miliyan 5, kuma zai buga wasanda Arsenal za ta fafata da Stoke ranar Lahadi da ma wassanin cin kofin zakarun turai.

Da ta ke jawabi bayan sun tashi da ci 3-3 da Liverpool, Wenger ya ce " Elneni ya komo cikinmu kuma zamu gani ko zai iya murza leda a fafatawar da za mu yi ranar Lahadi".

Elneny ya buga wassan da Basel ta buge chelsea a kakkar wassanin shekarar 2013-2014.