Klopp ya kare sukar da ake yi wa Mignolet

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Liverpool tana mataki na tara a kan teburin Premier da maki 31

Jurgen Kloop ya kare sukar da magoya bayan Liverpool ke yi wa mai tsaron raga Simon Mignolet kan sake da ya yi a karawar da suka yi da Arsenal.

Liverpool da Arsenal sun tashi 3-3 a gasar Premier wasan mako na 21 da suka buga a Anfield ranar Laraba.

Magoya bayan Liverpool suna zargin Mignolet da barin kwallaye biyu suka shiga raga a cikin sauki, kan cewa ya kamata ya hana su shiga.

Kloop ya ce musamman kwallo ta biyu da aka ci Liverpool ya kamata ace dukkan 'yan wasa sun taimaka hanata shiga ragar.

Haka ma a karawar da Liverpool ta tashi 2-2 da Exeter a gasar cin kofin FA an zargi mai tsaron ragar Liverpool din da yin sakaci a fafatawar.

Mignolet, mai shekara 27 dan wasan tawagar Belgium, na daf da saka hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a Anfield.