Sunderland ta dauko Dame N'Doye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland za ta fafata da Tottenham a gasar Premier ranar Asabar

Sunderland ta dauko Dame N'Doye daga kungiyar Trabzonspor, domin ya buga mata wasanni aro zuwa karshen kakar bana.

Dan wasan mai shekara 30 dan kasar Senegal ya buga wa Hull City tamaula a bara, inda ya ci kwallaye biyar daga nan ya koma Turkiya da murza leda.

Dan kwallon na jiran samun takardun izinin taka leda a Ingila, wanda hakan ba zai bashi damar buga wasan da Sunderland za ta yi da Tottenham ba a gasar Premier ranar Asabar.

N'Doye wanda zai saka riga mai lamba 10 shi ne dan wasa na biyu da Sunderland ta dauko bayan Jan Kirchhoff daga Bayern Munich.