Chelsea za ta iya nitsewa - Hiddink

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hiddink ya maye gurbin Mourinho

Kocin riko na Chelsea, Guus Hiddink ya ce suna fuskantar barazanar nitsewa daga gasar Premier zuwa ta Championship.

A yanzu dai Chelsea na matakin na 14 a kan tebur, kuma wasanninta biyu na gaba za ta kara ne da Everton da kuma Arsenal.

"Da gaske, wasanninmu biyu na gaba na da wuya," in ji Hiddink.

Maki shida ne ya raba Chelsea da kungiyoyin da za su iya nitsewa.

Wasannin karshen mako:

Asabar:

  • Tottenham v Sunderland
  • Bournemouth v Norwich
  • Chelsea v Everton
  • Man City v Crystal Palace
  • Newcastle v West Ham
  • Southampton v West Brom
  • Aston Villa v Leicester

Lahadi:

  • Liverpool v Man Utd
  • Stoke v Arsenal