Leicester za ta sayi dan Ghana Amartey

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin wannan watan ake sa ran kammala cinikin Daniel Amartey

Leicester City na tattaunawa da FC Copenhagen kan sayen dan Ghana Daniel Amartey.

Dan shekaru 21, zai iya buga wasa a tsakiya ko kuma a baya.

Rahotanni sun ce zai koma Leicester a kan fan miliyan shida.

Amartey ya buga wa Ghana wasa sau shida, kuma a baya ya murza leda a kungiyar Djurgarden ta Sweden.

Kocin Leicester, Claudio Ranieri ya siyo Demarai Gray daga Birmingham City a farkon wannan watan.

A yanzu dai Leicester ce ta biyu a kan teburin gasar Premier inda yawan kwallaye ya raba ta da Arsenal.