Southampton ta dauki Charlie Austin

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Queens Park Rangers ta bar buga gasar Premier a bara

Southampton ta dauko Charlie Austin dan kwallon Queens Park Rangers kan kudi da ake cewar ya kai fam miliyan hudu.

Austin ya ci wa QPR kwallaye 18 a gasar Premier a bara, hakan ya sa Ingila ta kira shi cikin tawagar 'yan kwallonta.

Dan wasan ya ci kwallaye 10 a wasanni 16 da ya buga wa QPR mai buga gasar Championship, kuma yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar bana.

Austin na yin jinya wanda rabon da ya buga wa QPR wadda ke matsayi na 17 a kan teburin gasar Championship wasa tun cikin watan Disamba.