CHAN 2016: Jamhuriyar Congo ta doke Habasha 3-0

Image caption Rwanda ce ke karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasan da ke murza leda a Afirka

Jamhuriyar Congo ta doke Habasha da ci 3-0 a gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasan da suke taka leda a Afirka da ake yi a Rwanda.

Jamhuriyar Congo wadda ke rukuni na biyu ta zura kwallayenta uku ne ta hannun Guy Lusadisu da Heritier Luvumbu da kuma Elia Meschack.

Sai a ranar Litinin ne rukuni na uku zai fara buga wasanninsa tsakanin Tunisia da Guinea da kuma karawa tsakanin Nigeria da Nijar.

A ranar Asabar aka fara buga gasar cin kofin Afirka ta 'yan kwallon da ke yin wasa a gida, inda Rwanda ta doke Ivory Coast da ci 1-0, Gabon da Morocco suka tashi wasa 0-0