Dan Aminu Langa-Langa ya buge Shagon Mada

Image caption Takawa tsakanin Dan Aminu Langa-Langa da Shagon Mada

Wasanni da dama aka dambata a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria a fafatawar da aka yi ranar Lahadi da safe.

A cikin wasannin ne Dan Aminu Langa-Langa daga Arewa ya kashe Shagon Mada daga Kudu a turmi na biyu.

Image caption Dan Kanawa da Dan Aliyu Shagon Langa-Langa

Kafin karawa tsakanin Dan Aminu da Shagon Mada, Bahagon Dan Kanawa ne ya buge Dan Aliyu Shagon Langa-Langa shi ma a turmi na biyu.

Shi kuwa damben Kurarin Kwarkwada daga Kudu da Nura Dan Karami daga Arewa zubar gade aka yi, shi Nura Dan Karami da duka, amma haka suka je kasa da Kurarin da aka doka.

  • Ga jerin wasannin da ba a yi kisa ba:
  • Shagon Autan Faya daga Kudu da Shagon Buzu daga Arewa
  • Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu da Shagon Alhazai Mai Kura daga Arewa
  • Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Dan Inna daga Kudu
  • Shagon Dan Jamilu daga Arewa da Shagon Bahagon Fandam daga Kudu
  • Shagon Soja daga Arewa da Bahagon Taye daga Kudu.