Arsenal tana mataki na daya a teburin Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana da maki 44 a matsayi na daya a kan teburin Premier

Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier duk da tashi wasa babu ci da suka yi da Stoke City a gasar a ranar Lahadi.

Wasan ya zama zakaran gwajin dafi ga Arsenal idan har za ta iya lashe kofin Premier na bana.

Stoke ta doke Arsenal da ci 3-2 a kakar gasar Premier ta bara, lokacin da Arsenal din ta ziyarci Stoke din.

Bayan da aka buga wasanni 22, Arsenal din ta lashe wasanni 13, an kuma doke ta sau hudu, sannan ta buga canjaras a karawa biyar.

Arsenal tana mataki na daya a kan teburi da maki 44, wadda rabonta da kofin Premier tun kakar 2003/04.