CHAN 2016: Nigeria ta doke Nijar 4-1

Hakkin mallakar hoto TheNFFTwitter
Image caption Nigeria ce ta daya a rukuni na uku da maki uku

Nigeria ta ci Nijar 4-1 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da suke murza-leda a Afirka da ake yi a Rwanda.

Nigeria ce ta fara cin kwallo ta hannun Osas Okoro bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, sannan ta kara ta biyu ta hannun Chisom Elvis Chikatara.

Nijar ta farke kwallo daya ta hannun Adebayor Zakari saura minti tara a tashi daga karawar.

Nan da nan Nigeria ta kara cin kwallaye biyu ta hannun Chisom Elvis Chikatara wanda ya ci uku a karawar.

Wasan farko na rukuni na uku da aka yi tsakanin Tunisia da Guinea sun tashi 2-2.