An yi wa Enyimba fashi da makami

Image caption Enyimba ce ta lashe gasar Firimiyar Nigeria da aka kammala

An yi wa kungiyar Enyimba fashi da makami a Okene da ke jihar Kogi a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna domin buga gasar Super Four.

'Yan fashin sun kwace kayayyakin 'yan wasa da jami'an kungiyar, amma ba a samu hasarar rayuka ko kuma jikkata 'yan kwallon ba.

Hukumar gudanar da gasar Premier ce ta tsara fara buga gasar Super Four da za a fara a ranar 20 ga watan Janairu a Kaduna.

Kungiyoyi hudun da za su fafata a gasar sun hada da Warri Wolves da Akwa United da Enyimba da kuma Nasarawa United.

A watan Maris din shekarar 2015, an yi wa 'yan Kano Pillars fashi da makami a Abaji da ke Abuja a kan hanyarsu ta zuwa Owerri inda aka raunata wasu 'yan wasanta biyar.