Leicester na daf da sayen Amartey na Ghana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester City tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Leicester City na daf da sayen dan kwallon tawagar Ghana, Daniel Amartey daga kungiyar FC Copenhagen.

Gidan rediyon BBC da ke Leicester ya bayar da rahoton cewar kudin da za a sayo dan wasan zai kai tsakanin fam miliyan biyar zuwa shida.

FC Copenhagen ta sanar da cewar karasa rattaba hannu kan takardun yarjejeniya ne suka rage a tsakanin kungiyoyin biyu.

Amartey -- wanda ya buga wa tawagar Ghana wasanni shida -- ya yi wa FC Copenhagen wasanni 63 tun lokacin da ya koma can a 2014.

Dan wasan shi ne na biyu da Leicester ta dauka a Janairun nan, bayan da ta fara sayo Demarai Gray daga Birmingham City kan kudi sama da fam miliyan uku.